Hadith for the World
FALALOLI DA LADUBBA

Ladaban Shari'a

67 hadiths

67 hadiths

Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce: "Shin kun san mece ce gibah?", suka ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani, sai ya ce: "Ka ambaci ɗan uwanka da abin da yake ƙi", aka ce: Shin kana ganin in ya kasance akwai abin da nake faɗa a kan ɗan uwana fa? sai ya ce: "Idan ya kasance a cikinsa akwai abin da kake faɗa, to, haƙiƙa ka yi gibarsa, idan babu (abin da kake faɗa) a cikinsa, to, haƙiƙa ka ƙirƙirar masa ƙarya".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abdullah bin Masoud - Allah ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - Salati da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan kun kasance uku, to biyu ba za su yi ma'amala ba tare da dayan ba, har sai kun cakuda da mutane, saboda wannan yana sa shi bakin ciki."Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abu Hurairah - Allah ya yarda da shi - tare da isnadi: “Bari saurayi ya gaishe da tsofaffi, masu wucewa, da‘ yan kadan a kan da yawa. ”Kuma a cikin ruwaya:“ Wanda ya hau kan mai tafiya.Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Ali bin Abi Dalib - Allah ya yarda da shi - da isnadi: “Idan dayanku ya yi sanadi, to ya fara da dama, idan kuma aka cire shi to ya fara da hagu, kuma bari hannun dama ya kasance na farkonsu ya kwance, kuma na karshe daga cikinsu ya cire”.Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abu Ayyuba Al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ba ya halatta ga mutum ya ƙauracewa ɗan uwansa sama da dare uku, suna haɗuwa, sai wannan ya kau da kai, wannan ma ya kau da kai, mafificinsu (shi ne) wanda zai fara yin sallama".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah ba Ya duba zuwa wanda ya ja tufansa (ƙasa) dan girman kai".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abdullah bn Amr bin Al-Aas - Allah ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Daya daga cikin manyan zunubai shi ne mutum ya zagi iyayensa." Aka ce: Shin mutumin yana zagin iyayensa ne? Sai ya ce: Ee, ya zagi mahaifin mutum, ya zagi mahaifinsa, mahaifiyarsa kuma ta zagi mahaifiyarsa.Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abdurrahman dan Abu Laila ya ce: Ka'abu dan Ujra ya hadu da ni, sai ya ce: Shin ba na baka wata kyauta ba? Lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya futo wurinmu, sai muka ce: Ya Manzon Allah, hakika mun san ya zamu yi maka sallama, to yaya zamu yi maka salati? Ya ce: "Ku ce: Ya Allah ka yi salati ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad, kamar yanda Ka yi salati ga (Annabi) Ibrahim da alayen (Annabi) Ibrahim, lallai cewa kai abin yabo ne kuma Mai girma. ya Allah Ka yi albarka ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad, kamar yadda ka yi albarka ga (Annabi) Ibrahim da alayen (Annabi) Ibrahim, lallai kai abin yabo ne kuma Mai girma".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
An rawaito daga Anas -Allah yayarda da shi- cewa shi ya ce da Sabit -Allah ya yi masa rahama: bana yo maka Rukya ba da rukyar Manzon Allah -Amincin Allah a gareshi-? ya ce E , yace: "Ya Ubangiji Mai renon Mutane, mai tafiyar da cuta, ka warkar kaine mai warkawa, babu mai warakarwa sai kai, warakarwar da bata barin cuta"Buhari ne ya rawaito shi
An rawaito daga Sauban -Allah ya yarda da shi- daga Annabi -Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya ce: "Lallai Musulmi idan ya gaida Dan Uwansa Musulmi yana cikin fukakukan Al-jannah har sai ya dawo, aka ce ya manzon Allah Me nene Khurfar Al-jannah? ya ce: Fukafukanta"Muslim ne ya rawaito shi
عن أنس بن مالك رضي الله عنه عن رسول الله صلى الله عليه وسلم أنه كان إذا أكل طعاما، لعق أصابعه الثلاث. قال: وقال: «إذا سقطت لُقمة أحدكم فليُمِطْ عنها الأذى، وليأكلها ولا يَدَعْهَا للشيطان» وأمر أن تُسْلَتَ القَصْعَةُ، قال: «فإنكم لا تدرون في أيِّ طعامكم البركة» وعن جابر بن عبد الله رضي الله عنه أن رسولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم قالَ: "إنّ الشيطانَ يَحضُرُ أحدَكُم عندَ كلِ شيءٍ من شَأنِه، حتى يَحضُرَهُ عندَ طعامِهِ، فإذا سَقطتْ لقمةُ أحدِكُم فليَأخُذْها فَلْيُمِطْ ما كانِ بها من أذى، ثم ليَأكُلْها ولا يَدَعْها للشيطانِ، فإذا فَرَغَ فليَلْعَقْ أصابعَهُ، فإنه لا يَدري في أيِّ طَعامه البركة"حديث أنس رواه مسلم. حديث جابر رواه مسلم
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai cewa kwatankwacin ma’abocin Alƙur'ani kamar kwatankwacin ma'abocin dabaibayayyun raƙuma ne, idan ya kula da su sai ya riƙesu, idan kuma ya sakesu sai su tafi".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
An rawaito daga Anas -Allah ya yarda da shi- "cewa shi ya wuce Yara sai yayi musu sallama, ya ce Annabi ya kasance yanayin hakanBukhari da Muslim suka Rawaito shi
An rawaito daga Abu huraira -Allah ya yarda da shi -daga Annabi: "Duk wanda aka bashi Raihan, to kada yaki karba, saboda yana saukin dauka, ga kuma dadin Kamshi"Muslim ne ya rawaito shi
Daga Anas Ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Lalle Allah Yana yarda da bawanda idan ya ci abin ci, yana gode masa a kai, ko in ya sha abin sha sai ya gode masa akan hakan.Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da su -: Cewa wani mutum ya tambayi Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi: Wanne aiki ne ya fi a Musulunci? ya ce: "Ka ciyar da abin ci, ka yi sallama ga wanda ka sani da wanda baka sani ba".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Ya Ubangiji ina neman tsari da kai daga yinwa, saboda cewa ita ce mafi muni daga..., kuma ina neman daga kai daga Ha'inciBukhari da Muslim suka Rawaito shi
عن جابر رضي الله عنه قَالَ: كُنَّا إِذَا صَعِدْنَا كَبَّرْنَا، وَإِذَا نَزَلْنَا سَبَّحْنَا. عن ابن عمر رضي الله عنهما قالَ: كانَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم وجيُوشُهُ إِذَا عَلَوا الثَّنَايَا كَبَّرُوا، وَإِذَا هَبَطُوا سَبَّحُوا.حديث جابر -رضي الله عنه- رواه البخاري. حديث ابن عمر -رضي الله عنهما- رواه أبو داود
عن علي رضي الله عنه قال: سمعتُ رسولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم يقول: « مَا مِنْ مُسْلِم يَعُودُ مُسْلِماً غُدْوة إِلاَّ صَلَّى عَلَيْهِ سَبْعُونَ ألْفَ مَلَكٍ حَتَّى يُمْسِي، وَإنْ عَادَهُ عَشِيَّةً إِلاَّ صَلَّى عَلَيْهِ سَبْعُونَ ألْفَ مَلَكٍ حَتَّى يُصْبحَ، وَكَانَ لَهُ خَرِيفٌ في الْجَنَّةِ».رواه أبو داود والترمذي وابن ماجه وأحمد
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya rantse sai ya ce a cikin rantsuwarsa: Na rantse da Lata da Uzza, to ya ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, wanda ya ce wa abokinsa: Zo mu yi caca tare, to ya yi sadaka".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbbat a gare shi - yana cewa: "Allah Ya ni'imtar da mutumin da ya ji wani abu daga gurimmu sai ya isar da shi kamar yadda ya ji, da yawa wanda aka isarwa yana zama mafi kiyayewa daga wanda ya ji".Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi
Daga Abi huraira Allah ya yarda dashi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce: "Bai Kamata Musulmi ya zamanto mai yawan tsinuwa ba"Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- : cewa Manzon Allah SAW ya ce: "Idan Mutum ya ce Mutane sun halaka, to shi ne ya halaka su".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amnicin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kada wani mutum ya kalli al'aurar wani mutum, ko mace ta kalli al'aurar wata mace, kuma kada wani namiji ya lulluɓa da wani mutum a cikin mayafi ɗaya, kuma kada wata mace ta lullaɓa da wata mace cikin mayafi ɗaya".Muslim ne ya rawaito shi